Tennis - 
Wallafa labari : Talata 12 Yuni 2012 - Bugawa ta karshe : Talata 12 Yuni 2012

Rafael Nadal ya lashe kofin Roland Garros

Dan kasar Spain Rafael Nadal a lokacin da ya ke daga kofin shi na bakwai a gasar Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa
Dan kasar Spain Rafael Nadal a lokacin da ya ke daga kofin shi na bakwai a gasar Roland Garros da ake gudanarwa a Faransa
REUTERS/Benoit Tessier

Daga Awwal Ahmad Janyau

Rafael Nadal ya lashe kofin Roland Garros, gasar French Open da ake gudanarwa a Faransa a karo na bakwai bayan ya lallalsa Novak Djokovic a wasan karshe da aka kwashe kwana biyu ana gudanarwa saboda ruwan sama. Nadal shi ne mutum na farko da ya lashe kofin gasar sau Bakwai.

Novak Djokovic dai a bana ya yi fatar lashe grand slams ne guda hudu bayan ya lashe Wimbledon, US Open da Australian Open

Ruwan sama da aka tabka a birnin Paris a ranar Lahadi shi ne ya kawo tsaikun kammala wasan karshe a fafatawar Novak Djokovic da Rafel Nadal, inda aka dage wasan zuwa ranar Litinin.

Novak Djokovic dai shi ne na daya a duniya kuma Rafeal Nadal ne ke bi masa a matsayin na biyu.

Sai dai Djokovic bai taba samun galabar Nadal ba a Rolanda Garros amma ya lallasa Nadal sau uku a wasu wasannin karshe da suka fafata.

Djokovic ne dai ya yi waje da Roger Federer a wasan kusa da karshe, kuma ya rama kashin da ya sha ne hannun Ferderer a bara.

A ranar Assabar ne a karon Farko Maria Sharapova ‘Yar kasar Rasha ta lashe kofin gasar Rolland Garros ta French Open da ake gudanarwa a kasar Faransa bayan ta doke Sara Errani ta Italiya.

Sharapova dai yanzu ta shiga sahun mata 10 suka lashe Roland Garros bayan ta lashe kofin Wimbledon da Us Open da Australian Open.
 

tags: Roland Garros - Tennis - Wasanni
KAN MAUDU'I GUDA
Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana
The content of this field is kept private and will not be shown publicly.
To prevent automated spam submissions leave this field empty.
CAPTCHA
This question is for testing whether you are a human visitor and to prevent automated spam submissions.
Close