Wasanni - 
Wallafa labari : Talata 07 Feberairu 2012 - Bugawa ta karshe : Talata 07 Feberairu 2012

Djokovic da Barcelona sun lashe kyautar Laureus

Novak Djokovic dan kasar Serbia yana sumbatar kyautar Laureus  ta bana da ya karba a birnin London
Novak Djokovic dan kasar Serbia yana sumbatar kyautar Laureus ta bana da ya karba a birnin London
REUTERS/Paul Hackett

Daga Awwal Ahmad Janyau

Novak Djokovic fitaccen dan wasan Tennis ya karbi kyautar gwarzon dan wasan Laureus na bana a birnin London, kungiyar Barcelona ce kuma ta karbi kyautar kungiya fitacciya a duniya.

Novak Djokovic shi ne mutum na biyar a Tarihin Tennis wanda ya lashe kofin gasa sau uku a jere.

Djokovic dan kasar Serbia shi ne zakaran wasan Tennis a Duniya inda ya lashe fitattun gasar da ake gudanarwa wato Australian Open da Wimbledon da US Open.

Bukin kyautar da aka gudanar a birnin London ya samu halartar fitattaun ‘yan wasa a bangarorin daban daban.

Kuma wasansu da dama sun ce wasanin Olympic da za’a gudanar a birnin London a bana zai share sunan irin wasannin da aka gudanar a Sydney da Athens da Biejing.
 

tags: Kwallon Kafa - Tennis
KAN MAUDU'I GUDA
Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana
The content of this field is kept private and will not be shown publicly.
To prevent automated spam submissions leave this field empty.
CAPTCHA
This question is for testing whether you are a human visitor and to prevent automated spam submissions.
Image CAPTCHA
Enter the characters (without spaces) shown in the image.
Close