Kwallon kafa - 
Wallafa labari : Litinin 06 Feberairu 2012 - Bugawa ta karshe : Litinin 06 Feberairu 2012

Gabon da E/Guinea sun zama ‘yan kallo a gasar Cin kofin Afrika

Dan wasan kasar Cote d'Ivoire  Didier Drogba a Lokacin da suke karawa da kasar Equartorial guinea
Dan wasan kasar Cote d'Ivoire Didier Drogba a Lokacin da suke karawa da kasar Equartorial guinea
REUTERS/Luc Gnago

Daga Awwal Ahmad Janyau

kasar Ghana da Mali da Cote d’Ivoire da Zambia sun tsallake zuwa wasan kusa `da karshe. Mali da Cote d’Ivoire ne suka sallami masu daukar nauyi gasar Gabon da Equatorial Guinea a wasan quarter final.

A ranar Assabar ne kasar Cote d’IVoire ta doke Equatorial Guinea ci 3-0.

A jiya Lahadi ne kasar Mali ta doke Gabon a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan kammala mintinan wasan ana kunnen doki ci 1-1. Didier Drogba wanda ya zira kwallaye biyu a wasan Cote divoire da Equatorial Guinea yana a babban birnin kasar Gabon lokacin da aka fitar da kasar a gasar.

‘Yan wasan Black Stars na Ghana sun doke Tunisia ne ci 2-1 duk da cewa alkalin wasa ya ba d an wasan Ghana Jan kati.

Yanzu haka a ranar Laraba kasar Ghana zata fafata da Zambia wacce ta doke kasar Sudan a wasan Quarter final.

Cote d’Ivoire kuma zata kara ne da kasar Mali.
 

tags: Gasar Cin Kofin Africa - Kwallon Kafa - Wasanni
KAN MAUDU'I GUDA
Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana
The content of this field is kept private and will not be shown publicly.
To prevent automated spam submissions leave this field empty.
CAPTCHA
This question is for testing whether you are a human visitor and to prevent automated spam submissions.
Image CAPTCHA
Enter the characters (without spaces) shown in the image.
Close