Premier - 
Wallafa labari : Litinin 06 Feberairu 2012 - Bugawa ta karshe : Litinin 06 Feberairu 2012

Chelsea 3 United 3, Villas-Boas yace wannan shan kashi ne

'Yan wasan Manchester United "Chicharito" da Park da  Rooney a lokacin da suke murnan zira kwallo a ragar Chelsea.
'Yan wasan Manchester United "Chicharito" da Park da Rooney a lokacin da suke murnan zira kwallo a ragar Chelsea.
Reuters

Daga Awwal Ahmad Janyau

A gasar Premier League ta Ingila, wasa tsakanin Manchester United da Chelsea an tashi ne ci 3-3, Farkon fara wasan ‘yan wasan Ferguson sun kama hanyar shan kashi ne inda dan wasan shi Jonny Evans ya fara zirawa Chelsea kwallonta a raga kafin daga bisani kuma Juan Mata David Luiz suka sake saka wasu kwallayen biyu a raga.

Bayan dawowa rabin lokaci ne dai Wayne Rooney ya barke kwallaye biyu a bugun daka kai sai mai tsaron gida tare da Karin kwallon daya da Xavier Hernandez ya zira da kai.

Yanzu maki biyu ne tsakanin Manchester United da Manchester City da ke jagorancin Tebur inda tuni City ta lashe wasanta a ranar Assabar.

Kocin Cheslea Villas-Boas yace sakamakon wasan kamar shan kashi ne hannun United.
 

tags: Kwallon Kafa - Premier League
KAN MAUDU'I GUDA
Ra'ayoyi
Bada ra'ayi kan wannan magana
The content of this field is kept private and will not be shown publicly.
To prevent automated spam submissions leave this field empty.
CAPTCHA
This question is for testing whether you are a human visitor and to prevent automated spam submissions.
Image CAPTCHA
Enter the characters (without spaces) shown in the image.
Close