Wasanni

Syndicate contentWASANNI
Dan wasan Manchester United Rio Ferdinand
16/05/2012 - Ingila

Hodgson ya ajiye Ferdinand a tawagar Ingila zuwa gasar Turai

sabon kocin ‘Yan wasan Ingila, Roy Hodgson ya ajiye Rio Ferdinand cikin tawagar shi da zasu haska a gasar cin kofin Turai a kasashen Ukraine da Poland.

Francois Bocande Tsohon Dan wasan Senegal wanda ya mutu yana da shekaru 54
16/05/2012 - Senegal

Dubban mutanen Senegal sun karrama Bocande

A kasar Senegal daruruwan mutane ne suka yi gangami a babban filin wasan kwallon kafa a Dakar, domin karrama fitaccen dan wasan kwallon kafar kasar Francois Bocande wanda ya mutu a ranar 7 ga watan Mayu a kasar Faransa.

Wani hoton da aka hada tsakanin Messi da Ronaldo da Yaya Toure wanda kuma ke dauke da tambarin Rediyon Faransa da gidan Telebijin na France 24
15/05/2012 - Kwallon Kafa

An kammala Seria A da Premier da La liga da Bundesliga

Bayan kammala Seria A da Premier da La liga da Bundesliga, mun yi nazari game da kungiyoyin da suka lashe league league da kungiyoyin da zasu haska a gasar zakarun Turai da Europa a badi da kuma ...

Carlos Tevez yana da rike da kofin Premier tare da Roberto Mancini kocin Manchester City a lokacin da suka lashe kofin bayan doke QPR ci 3-2
14/05/2012 - Premier

Manchester City ta lashe kofin Premier

Manchester City ta karbe kofin Premier hannun Manchester United a bana bayan samun nasara a akan QPR ci 3-2 a wasannin karshe da aka gudanar na Premier.

Tsohon zakaran damben Boxing ajin masu nauyi David Haye na Birtaniya a lokacin da suke kokarin gwabzawa da Dereck Chisora a bayan fage bayan Chisora ya sha kashin hannun Vitali Klitschko a birnin Munich na kasar Jamus
10/05/2012 - Boxing

Hukumar Boxing a Birtaniya ta la’anci Damben kece raini tsakanin Chisora da Haye

Hukumar Damben Boxing a kasar Birtaniya ta la’anci Damben kece raini da aka shirya gudanarwa a watan Yuli tsakanin Dereck Chisora da David Haye, tare da gargadin daukar mataki akan duk wanda ya shirya gudanar da Damben.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Brazil, Ricardo Teixeira, yana gaisawa da ronaldo tsohon dan wasan Brazil a lokacin da zasu gudanar da wani taron kwamitin shirya gasar cin kofin Duniya da Brazil zata dauki nauyi a shekarar 2014.
10/05/2012 - Brazil

Majalisar Brazil ta amince a sayar da Giya a filin wasa

Majalisar Dattijai a kasar Brazil ta amince a sayar da giya a lokacin gudanar da gasar cin kofin Duniya, kamar yadda hukumar FIFA ta bukata duk da ’Yan adawa sun kalubalanci kudirin cikinsu har da Tsohon dan wasan kasar Romario.

Falcao dan wasan Atletico Madrid rike da Kofin Europa tare da abokan wasan shi bayan doke Bilbao
10/05/2012 - Europa league

Atletico Madrid ta lashe kofin Europa

Atletico Madrid ta lashe kofin gasar Turai na Europa League karo na biyu cikin shekaru uku, bayan ta lallasa makwabciyarta Athletic Bilbao ci 3-0.

Tsohon zakaran damben Boxing ajin masu nauyi David Haye na Birtaniya a lokacin da suke kokarin gwabzawa da Dereck Chisora a bayan fage bayan Chisora ya sha kashin hannun Vitali Klitschko a birnin Munich na kasar Jamus
09/05/2012 - Boxing

Chisora da Haye zasu yi Damben kece raini

A Birtaniya an tabbatar da Damben kece raini tsakanin Dereck Chisora da David Haye wanda za’a gudanar a watan Yuli saboda huce hushin juna.

Filin wasan da za'a buga wasa tsakanin Atletico Madrid da Athletic Bilbao a Bucharest kasar Romania
09/05/2012 - Europa league

Europa League: Atletico Madrid zata fafata da Athletic Bilbao a wasan karshe

A yau Laraba ne kungiyoyin Spain guda biyu Atletico Madrid da Athletic Bilbao zasu buga wasan karshe a gasar Turai ta Europa League a birnin Bucharest na kasar Romania. Atletico zata yi kokarin maimata tarihin nasarar da ta samu a shekarar 2010 inda ta doke Fulham ci 2-1 a wasan karshe.

'Yan wasan kungiyar Liverpool a Ingila
09/05/2012 - Premier

Liverpool ta rama kashin da ta sha hannun Chelsea

Kungiyar Liverpool ta rama kashin da ta sha hannun Chelsea a gasar FA domin a daren jiya Liverpool ta lallasa Chelsea ci 4-1 a Premier league. Yanzu kuma ya zama dole sai Chelsea ta lashe kofin gasar zakarun Turai a wasa tsakaninta da Munich kafin ta sake samun hurumin shiga gasar a badi.

Alamar wasannin Olympics na birnin London
08/05/2012 - Wasanni

Za a sayar da karin tikitin wasannin Olympics na birnin London

A ranar juma’a mai zuwa ake sa ran fara sayar da Karin tikitin wasanni Olympics na birnin London har kusan miliyon 1.

Logo de l'Euro 2012 de football.
08/05/2012 - Wasanni

Kasashe na ci gaba da shirin kauracewa wasannin Euro 2012 a Ukurain

A yau lahadi kasar Ukraine tace ta dakatar da taron da ta shiya na kasashen Turai, da a daa ta tsirya karbar bakuncin shi, a ranar juma’a mai zuwa, a shirye shirye fara wasannin cin kofin ...

Dan wasan Nigéria Yakubu Aiyegbeni a wasa Manchester United da Blackburn.
08/05/2012 - Premier

Blackburn Rovers ta fice Premier

Kungiyar Blackburn Rovers ta fice gasar Premier league bayan tasha kashi hannun Wigan Athletic ci 1-0. Blackburn ta kwashe shekaru 11 ana fafatawa da ita a Premier, amma Wigan ta sha da kyar ne domin fuekantar barazanar ficewa gasar.

'Yan wasan Montpellier
08/05/2012 - Kwallon kafa

Montpellier na gab da lashe kofin League na Faransa

Kungiyar Montpellier na gab da lashe kofin league din kasar Faransa bayan ta lallasa kungiyar Rennes ci 2-0, domin yanzu maki uku ne tsakaninta da PSG, saura kuma wasanni biyu a karkare gasar.

Alamar gasar cin kofin turai na Euro 2012.
07/05/2012 - Wasanni

Ukraine ta mayar da martani ga masu kiran a kaurace wa wasanni a Kasar

PM kasar Ukraine Mykola Azarov ya mayar da martani ga masu kliraye kirayen neman a kaurace wa wasannin gasar cin kofin nahiyar Turai da za a buga a kasar, saboda yadda ake gallaza wa tsohuwar PM Yulia Tymoshenko.

Wasu magoya bayan kungiyar Juventus mace da namiji rike da Tutar kungiyar suna sunbatar juna domin murnar lashe kofin Seria A bayan kammala wasa tsakanin Juventus da Cagliari
07/05/2012 - Kwallon kafa

Juventus ta lashe kofin Seria A, Manchester City na kusa da lashe Premier

Kungiyar Juventus ta lashe kofin Seria A bayan ta doke Cagliari a ranar Lahadi bayan AC Milan ta sha kashi a hannun Inter Milan, a Premer League kuma wasa daya ya rage a Manchester City ta lashe kofin gasar. Chelsea kuma ta lashe kofin FA bayan samu galabar Liverpool.

José Mourinho,Kocin  Real Madrid, a lokacin da yake ganawa da manema labarai
04/05/2012 - Kwallon Kafa

Mourinho yace gurin shi ya cika bayan lashe La liga da Seria A da Premier

Mourinho yace baya da wani sauran gurin aikin horar da wata kungiya a wata kasa bayan ya lashe manyan kofunan gasar kasashen Turai. Mourinho ya lashe kofin Premier da Chelsea, sannan ya lashe kofin Seria A da inter Milan sannan kuma yanzu ya lashe kofin La liga da Real Madrid bayan duk ya lashe kofin kasarsa Potugal da FC Porto.

Wayne Rooney Dan wasan  Manchester United
04/05/2012 - Premier

Rooney ya lashe kyautar wanda ya zira kwallon da ta fi Shahara a Premier

Wayne Rooney Dan wasan Manchester United shi ne ya lashe kyautar wanda ya zira kwallon da ta tafi shahara a raga a Premeir League. Rooney ya lashe kyautar ne sanadiyar wata kwallo da ya zira a ragar Manchester City da akro.

Guillaume Hoarau na  kungiyar PSG
03/05/2012 - Faransa

Maki uku ne yanzu tsakanin PSG da Montpellier

Kungiyar PSG a ta datse yawan makin da ke tsakaninta da Montpellier zuwa maki Uku daga Shida bayan PSG ta doke Saint-Etienne ci 2-0. Har yanzu Montpellier ce ke jagorancin Tebur da maki uku amma saura wasanin uku a kammala gasar Frecnh league.

Papiss Cisse dan wasan kungiyar Newcastle United a lokacin da yek murnar zira kwallo a ragar Chelsea
03/05/2012 - Premier

Newcastle ta samu galabar Chelsea a Stamford Bridge

A gasar Premier a Ingila Chelsea tasha kashi hannun Newcastle United ci 2-0, kuma kashin da Chelsea ta sha, damuwa ne a yunkurinta na samun hurumin shiga gasar zakarun Turai a badi.

Close