Isa ga babban shafi
Italiya

Sojan ruwan Italiya sun sake ceto bakin haure daga cikin teku

Sojan ruwan Italiya sun gunadar da wani akin ceton da suka fiddo bakin haure 4,200, da a lokacin da suke tafiya, cikin jiragen ruwa a kan tekun Meditareniya, cikin har da wasu 17 da suka mutu. Har zuwa daren jiya juma’a ana ci gaba da aikin ceton, sai dai kuma rundunar sojan ruwan bata gano abinda yayi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikin bakin hauren ba.Dama a baya hukumomin kasar ta Italiya sun bayyana yadda bakin hauren ke fuskantar matsanancin yanayi a kan teku, game da yunwa ga kuma fadace fadacen da suke yi da junan a cikin kwale kwalen dake shake da mutane, lamarin da ke sanadiyyar mutuwar su.Kasar Italya ce tafi kowacce kasa samun bakin haure dake kwarara daga kasashen Africa da nahiyar Asiya. 

Wani kwale kwale dauke da bakin haure a kan teku
Wani kwale kwale dauke da bakin haure a kan teku REUTERS/Olivia Harris
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.