Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta gargadi Indonesia kan kisan dan kasarta.

Shugaban Kasar Faransa Francois Hollande ya gargadi kasar Indonesia cewa kada ta kuskura ta aiwatar da hukuncin kisa kan wani Bafaranshe da aka samu da laifin fataucin miyagun kwayoyi

Serge Atlaoui a hannun jami'an tsaron Indonesia
Serge Atlaoui a hannun jami'an tsaron Indonesia GACAD/AFP
Talla

Hollande yace, aiwatar da hukuncin kisan zai bata dangantakar dake tsakanin Kasashen biyu.

Shima ministan harkokin wajen kasar Laurent Fabius ya gayyaci Jakadan kasar Indonesia dake Paris, inda ya bayyana masa bukatar kasar.

An dai yankewa Serge Atlaoui mai shekaru 51 ne hukuncin kisa saboda samun sa da laifin safarar miyagun kwayoyi bayan shafe tsawon shekaru kulle a gidan yari

Atlaoui dai mai yara hudu ya musanta laifin da aka ce ya aikata, inda kuma ya daukaka kara amma bai yi nasara ba.

A ‘yan kwanakin nan ne, dangin Atlaoui suka bukaci gwamnatin Shugaban Kasar ta Faransa, da Kungiyar kasashen Turai dasu taimaka wajan ceto shi daga hannun gwamnatin Indonesia.

Atlaoui zai kasance Bafaranshe na farko cikin shekaru 40 da aka yanke wa hukuncin kisa a ko ina a fadin duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.