Isa ga babban shafi
EU

EU na gudanar da taron akan matsalar bakin haure

Mahukumtan kasashen turai da suka soma gudanar da zaman taron su a yau alhamis, na kokarin samar da amsa mai karfi da za ta kawo karshen asarar rayukan bakin haure a gabar tekun Medetraniyan, matakin da ya hada da ayukan soja kan masu safarar bakin hauren, haka kuma su da kansu su nuna halayen dattako wajen karbar yan gudun hijira a kasashensu.

Shugabannin kungiyar tarayya turai da ke gudanar da taro akan bakin haure
Shugabannin kungiyar tarayya turai da ke gudanar da taro akan bakin haure REUTERS/Yves Herman
Talla

Kafin soma gudanar da zaman taron na yau Shugaban hukumar zartarwar kungiyar tarayyar turai Donald Tusk, ya bayyana cewa matsalar bakin haure ba matsala bace da za’a iya magancewa a wannan zaman taro nasu na yau da aka kira bayan faruwar mummunan hatsrin da yayi sanadiyar salwantar rayukan bakin haure 800 a tekun na medtraniyan

Abu mai wahala ga gwamnatocin na turai shine nuna samar da hadin kai a tsakaninsu, Tusk ya kara da cewa doli ne sai sun nuna da gaske suke yi wajen sadaukar da wasu muradun kasashensu domin magance matsalar

Wannan furucio dai irinsa ne shugaban gwamnatin kasar Girka, Alexis Tsipras ya yi ,.

Daya daga cikin kalubalan da zaman taron ke fuskanta shine nuna cewa da gaske suke yi wajen samar da hadin kai a tsakaninsu kan matsalar ta hanyar yin raba dai dai da bakin hauren a tsakanin kasashen nasu in ji pm kasar ta Girka

Kasar Girka da Italie da kuma tsibirin Malt sune kasashe 3 da ke ci gaba da karbar bakin hauren dake fitowa dfaga gabar ruwan kasar Libiya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.