Isa ga babban shafi
France-Lebanon

Faransa Ta Aike Da Kayan Yaki Lebanon

Kasar Faransa ta tura makamai na farko zuwa kasar Lebanon karkashin wata yarjejeniya da kasar Saudiyya ta dauki nauyi.Makaman na kudin Amirka Dolla biliyan uku za su isa Lebanon gobe littini kuma za'ayi amfani da makaman ne domin yakar kungiyar IS dake da'awar kafa daular Islama.Faransa zata samar da motocin yaki 250, da jiragen sama masu saukan ungulu na yaki 7, da wasu jiragen yaki na ruwa 3, da wasu tarin kayan yaki na zamani da za'a rika kaiwa kasar Lebanon sannu a hankali cikin shekaru hudu.  

Firaministan Lebanon Tammam Salam
Firaministan Lebanon Tammam Salam Reuters/Jamal Saidi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.