Girka
Girka Da Manyan Cibiyoyin Bada Bashi Na Taro a Paris
Wakilan kasar Girka da ayarin wakilan cibiyoyin bada rance na duniya ma wani taro yau a Paris domin tattauna batun dimbin basuka da ake bin kasar Girkan, da irin sauye-sauyen da ake bukata daga gareta muddin ta na bukatar ci gaba da tafiya da ita.Ya zuwa yanzu dukkan tattaunawa da akeyi da ita na nuna zai yi wuya ta iya biyan basukan kafin a taimaka mata.Taron na yau zai kunshi wakilan kungiyar tarayyar Turai, da wakilan Asusun Bada Lamuni IMF da kuma wakilan babban Bankin Turai.
Wallafawa ranar: