Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus

Akwatin nadar Maganar Jirgi Germanwings ya lalace

A yau laraba masu aikin ceto a kasar faransa sun sanar da gano bakin akwati nadar bayyanai jirgin da yayi hadari jiya, dauke da Mutane 150, irin sa mafi muni shekaru 30 a cikin kasar ta faransa.

Ana gudanar da aikin Ceto
Ana gudanar da aikin Ceto REUTERS/Robert Pratta
Talla

A yanzu dai an fara tarkato wasu tarkaccen jirgi da aka gano tare da bakin akwatin a kusa da inda hatsari ya auku sai dai wasu bayyanai na cewa Akwatin ya lalace, kuma tuni aka aike da shi birnin Paris domin bincike

Jirgin Germanwings, kirar Airbus 320 yayi hatsari ne kusa da wurin zamiyar kankara wato French Alps, a kudanci faransa bayan tasowar sa daga Barcelona
 

Kamfanin Jirgin saman ya tabbatar da cewar acikin Fasinjoji 144 da jirgin ke dauke dasu akasarin matafiyan ‘Yan asalin kasar jamus ne, wadanda 16 cikin su yan makaranta ne da basu haura shekaru 18 ba
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.