Isa ga babban shafi
Singapore

Al-ummar Singapore na cigaba da alhinin rashin Kuan Yew

Al-ummar Kasar Singapore na cigaba da alhinin rashin Firaministan Kasar na farko, Lee Kuan Yuen yayinda suka yi turuwa dan mika sakonnin ta'aziyarsu daya bayan daya

Wasu 'Yan Singapore a harabar Asibitin da Kuan Lee ya mutu
Wasu 'Yan Singapore a harabar Asibitin da Kuan Lee ya mutu REUTERS/Timothy Sim
Talla

Labarin mutuwar Kuan Yuen ya bazu ne, bayan dansa, wanda kuma shine Firaminsstan kasar na yanzu, Lee Hsien, ya gabatar da jawabi, inda ya sanar da rashin mahaifinsa mai shelaru 91, da ya gamu da ajalinsa a babban asibitin Singapore, bayan fama da doguwar jinya.

A jawabin nasa, Firaministan ya bayyana cewa, Kuan Yew ne, ya jajirce har kasar ta samu ‘yancin kai, kuma ya ginata tare da samar da cigaban al-ummar kasar, lamarin da ya sa firamisnisatan yace, ba zasu taba samun kwatankwacinsa ba.

A nashi bangaren, shugan Amurka Barrack Obama, ya jagoranci shugabannin kasashen duniya wajan jinjinawa marigayi Kuan Yew, inda yace, shine ya yi kokari har kasar ta samu cigaba a yanzu,

Tun shekara ta 2010 ne, Kuan Yew ya fusakanci tsannanin rashin lafiya, bayan mutuwar Uwargidansa Kwa Geok, mai shekaru 63.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.