Isa ga babban shafi
Faransa

Kotun Faransa ta hukunta dan wasan Barkonci saboda Yahudawa

Kotun faransa ta ci tarar Diedonne, dan wasan barkocin nan, Euro dubu 22 da 500, sakamakon furucin batanci da yayi ga yahudawa cikin barkonci  

Dan Wasan Barkoncin Faransa, Dieudonne
Dan Wasan Barkoncin Faransa, Dieudonne veteranstoday.com
Talla

A karo na biyu kenan cikin mako guda, da Diedonne Mbala ya gurfana a gaban alkali kuma aka yanke masa hukunci, sakamon kalaman da ya furta na batanci ga yahudawa, da ake tunanin kan iya haifar da kiyayya a garesu.

Gazawarsa wajan biyan wadannan kudadan da aka ci shi tara, kan yi dalilin tsawaita zamansa gidan yari.

Diedonne ya taka dokar faransa data yi hani ga furta kalaman da zasu iya haifar da kyamar wani a zukatan al-umma, yayinda kuma, yayi burin mutuwar wani Bayahude dan jarida mai suna Patrick Cohen.

A ranar larabar data gabata ne, Diedonne, ya fara gurfana a gaban Kotu kuma aka yanke masa hukunci zaman watanni 2 a gidan Maza, bayan an same shi da laifin sanya bayanai a shafukan sada zumunta, inda ya nuna alamar jajantawa ‘yan bindigan da suka kashe yahudawa hudu a ranar 9 ga watan janairu, a babban shagon Kosher, dake birnin Pari, yayinda sau bakwai kenan, da aka same shi da laifin kokarin cusa kiyayyar yahudawa ga jama’a.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.