Isa ga babban shafi
Spain-Ukraine

Spain na tsare da Ministan kudin Ukraine

Wata Kotun kasar Spain ta bayar da umarnin ci gaba da tsare tsohon ministan kudin kasar Ukraine Yuri Kolobov, har zuwa lokacin da za a mika shi ga hukumomin birni Kiev, inda ake neman shi don amsa zargin zamba cikin aminci, da satar kudaden gwamnati.

Yuri Kolobov
Yuri Kolobov ipress.ua
Talla

Ranar Laraba ta da gabata ‘yan sanda suka tsare Mr. Kolobov, wanda shi ne minista a zamanin gwamnatin hambararren shugaba Viktor Yanukovych, kuma gwamnatin Ukraine na da kwanaki 40 da za ta iya mika takardun neman a mika shi.

Kolobov, mai shekaru 41 a duniya ne aka fara cafkewa a jerin ministocin hambararriya gwamnatin Yanukovych, mai goyon baya Rasha.

Yau juma’a kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya zai yi zama na musamman don duba kokarin kawo karshen rikicin da ke faruwa a gabashin kasar Ukraine.

Jami’an diplomasiyya sun tabbatar da taron, kuma kwamitin tsaro mai mmbobi 15 ya amince da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cim ma tsakanin Rasha da Ukraine, inda kasashen Faransa da Jamus suka sa ido a kai, don kawo karshen rikicin.

Yakin kasar ta Ukraine, da aka shafe watanni 10 ana gwabzawa, shi ne Rikici mafi muni a Turai tun bayan yakin Balkans da aka yi cikin shekarun 1990.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.