Isa ga babban shafi
Rasha

An yi zanga zangar tunawa da madugun 'yan adawa da aka kashe a Rasha

Jiya Lahadi dubun dubatar ‘yan kasar Rasha sun yi gangami a tsakiyar birnin Moscow, don girmama madugun ‘yan adawan kasar Boris Nemtsov, da aka bindige a tsakiyar birnin. A daren ranar Juma’a, wasu da ba a san ko su waye ba, suka harbi Nemtsov mai shekaru 55 a baya.Wannan ne gangamin da ake ganin ya fi kowanne tara jama’a tun wanda aka cikin shekarun 2011 zuwa 2012, inda aka ga dandazon muatne da suka kai dubu 100.‘Yan adawn kasar sun ce mutane dubu 70 ne suka watsu kan titunan birnin Moscow, don karrama Boris Nemtsov, sai dai ‘yan sanda sun ce masu zanga zangar basu wuce dubu 21 ba.Mutanen, dauke da tutar kasar da kyallaye sun taru a wani dandali, inda suka yi Allah wadi da hukumomin birnin Moscow, kafin daga bisani su nausa zuwa kan wata gada, inda aka bindige dan adawan.Wasu daga cikin ‘yan kasar sun yi amfani da zanga zangar wajen nuna adawa da yakin kasar Ukraine, da ake zargin Rashan da hannu a ciki.Wasu mutane da suka kai dubu 6, wasu lullube da tutar kasar Ukraine, sun yi nasu gangamin a Saint Petersburg, birni na 2 mafi girma a kasar ta Rasha.Dama jiya lahadin marigayi Boris Nemtsov ya shirya jagorantar zanga zanagar nuna adawa da rawar da ake zargin Rasha na takawa a rikicin kasar Ukraine. 

'Yan kasar Rasha dake zanga zangar tunawa da Boris Nemtsov, a birnin Moscow
'Yan kasar Rasha dake zanga zangar tunawa da Boris Nemtsov, a birnin Moscow REUTERS/Sergei Karpukhin
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.