Isa ga babban shafi
Syria-Faransa

Rikicin Syria ya yi sanadiyyar rabuwar kanun 'yan siyasan Faransa

An fara samu rabuwar kanun ‘yan majalisun kasar Faransa dangane da rikicin kasar Syria. Wannan na zuwa ne kwanaki biyar bayan ganawar wasu daga cikin yan majalisun kasar da shugaba Bashar al-Assad.Rabuwar kanun na zuwa dangane da matakan daya dace Faransa ta dauka, kan shugaba Bahsar al-Assad, wanda hukumomin birnin Pari suka ce yana yi wa ‘yan kasar shi mulkin kama karya Ko a mskon daya gabata sai da shugaba Francois Hollande ya soki ganawar da wasu ‘yan majalisun kasar suka yi da shugaba Assad.inda ya ce bai dace ‘yan majalisun su gana da shugaban da ya yi sanadiyar barkewar yakin basasa a kasarsa ba.Shugaba Hollande yace Faransa ba zata shiga tattaunawa da shugaban da ya yi anfani da makamai masu guba wajen hallaka al’ummarsa ba, maimakon kare su.‘Yan majalisu uku daga wasu jam’iyoyin kasar ne suka kai wa shugaba Assad ziyara tare da ganawa da wasu manyan ministocin kasar ta Syria.Faransa dai ta yanke dangata da Syria a shekara ta 2012, yayin da kasar ta goyi bayan tsige shugaba Assad daga karagar mulki. 

Shugaban Faransa, François Hollande
Shugaban Faransa, François Hollande
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.