Isa ga babban shafi
Faransa

Dan jaridar Al jazeera zai gurfana a kotun Paris

Majiyoyin kotu a kasar Faransa sun bayyana cewa a makon gobe ne za a fara sauraron karar da aka shigar na daya daga cikin ‘yan jaridun tashar Aljazeera uku da ake zargi sun yi shawagi da jiragen sama birnin Paris wadanda babu kowa a ciki.

REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Dan jaridar tuni ya amsa cewa shi ne ya tura kurman jirgi da ya yi ta shawagi sararin samaniyar Paris a ranar Laraba.

Da farko an kama dukkan ‘yan jaridun ne uku amma aka saki biyu daga baya.

Shawagin kurman jirgi katon laifi ne a Faransa, domin koda cikin watan 10 na bara wani dan Isra’ila mai shekaru 24 da ke yawon shakatawa a Faransa sai da aka daure shi na kwana guda sannan kuma ya biya taran kudi yuro 400 saboda cilla wani abu mai kama da jirgin sama da babu kowa ciki.

Dan jarida da ke aiki da tashar Aljazeera, dan shekaru 34, dan asalin Birtaniya ne, wan ya sarrafa karamin kurman jirgin da wata na’ura da ke hannunsa a inda ya ke tsaye da sauran ‘yan jaridu biyu.

Jamian tsaro na Faransa dai sun kwace jirgin da tarkace nauran.

Tashar Aljazeera tace ‘yan jaridun na gwajin na’urorin daukan hoto ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.