Isa ga babban shafi
Faransa

EU ta ba Faransa wa’adi zuwa 2017

Kungiyar Tarayyar Turai ta ba Faransa nan da shekarar 2017 ta datse kasafin kudinta ko kuma a ci ta tara. Hukumar ta fitar da sanarwar ne a birnin Brussels tare da bayyana cewa dole ne Faransa ta mutunta ka’idojin kungiyar da suka bukaci illahirin kasashen yankin da su tabbatar da cewa gibin kasafin kudinsu bai haura kashi uku cikin dari ba.

Shugaban Faransa Francois Hollande
Shugaban Faransa Francois Hollande Reuters/路透社
Talla

Wa’adin da kungiyar ta bayar zai kare ne a lokacin da Faransa ke gudanar da zaben shugabancin kasa, wanda Francois Hollande zai bukaci wa’adi na biyu a shekara ta 2017.

Faransa dai na a matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a yankin na Turai, kuma ci gaba da samun gibi a kasafin kudinta abu ne da masana tattalin arziki ke cewa yana shafar yankin da kuma darajar takardar kudin Euro.

To sai dai kwamishinan kudi na kungiyar ta Turai Pierre Moscovici wanda tsohon ministan kudin Faransa ne, ya ce suna fatan lamarin ba zai kai ga cin kasar tara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.