Isa ga babban shafi
Austria

Austria ta haramtawa Musulmi samun tallafi

Majalisar Kasar Austria ta amince da wata sabuwar dokar hana kungiyoyin Musulmin kasar samun tallafin kudade daga kasashen waje tare da kuma tilastawa Liammai koyan harshen Jamusanci. Wannan sabuwar doka da ministan harkokin cikin gidan Austria Sebastian Kurz ya kira ta a matsayin Musuluncin Turai an yi ta ne don dakile tasirin ra’ayoyin Musulmin kasashen duniya a cikin kasar.

Kofar ajiyar kudi a wani bankin kasar Austria a Vienna
Kofar ajiyar kudi a wani bankin kasar Austria a Vienna REUTERS/Heinz-Peter Bader
Talla

Dokar ta kuma kara bai wa al’ummar Musulmin kasar ‘yancin gudanar da addininsu ba tare da wata tsangwama ba.

Sai dai dokar ta gamu da suka daga sassa dabam dabam, cikin su har da Musulmin kasar da ke shirin kalubalantar dokar a kotu.

Ko a watan jiya shugaban Amurka Barack Obama ya bukaci janyo al’ummar Musulmi a jika maimakon yadda ake nuna musu kyama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.