Ministocin Turai sun aminta a karawa Girka wa’adi
Ministocin Kungiyar kasashen Turai masu amfani da kurin yuro sun yi na’am da sabbin sauye sauyen da kasar Girka ta gabatar domin neman karin wa’adin watanni hudu kan bahsin da ake bin kasar. Sai dai Hukumar bayar da lamuni ta duniya da Babban Bankin kasashen Turai na dari-dari da sabon tsarin na Girka.
Wallafawa ranar:
Girka ta gabatar da sabbin tsare tsaren ne a ranar Litinin kuma Ministocin kasashen na Turai 19 sun amince da sabon tsarin bayan sun tattauna ta wayar Tarho.
Amma dole sai Majalisar kasashen na Turai ciki har da Jamus da ke matsin lamba ga Girka sun amince da sabbin sauye sauyen kafin wa’adin da aka dibar wa kasar tun da farko ya kawo karshe a ranar Assabar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu