Isa ga babban shafi
Girka

Girka ta mika sabbin sauye-sauyenta ga Turai

Kasar Girka ta gabatar da sabbin sauye-sauyenta zuwa Brussels a yau Talata, kamar yadda kungiyar kasashen Turai ta bukata domin ba iwa kasar Karin lokacin biyan dimbin bashin da ake bin ta. Girka na neman karin wa’adin watanni hudu amma sai masu bayar da bashi sun amince.

Firaministan kasar  Girka Alexis Tsipras
Firaministan kasar Girka Alexis Tsipras REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Daga cikin sabbin tsare-tsaren da Girka ta gabatar akwai batun yaki da ma su kaucewa biyan haraji da masu fasa kwabrin man fetur da taba sigari cikin kasar.

Dole sai masu bin kasar ba shi sun amince da shirin kafin a amince da Karin watanni hudu don ta biya bashin da ake bin ta.

Hukumomin da zasu yi nazari kan sabbin sauye-sauyen sun hada da hukumar Turai da Babban Babban Turai da kuma asusu bayar da lamuni wadanda ke bin kasar Bashi kudi da suka kai yuro biliyan 320.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.