Isa ga babban shafi
Faransa

An kwace takarudun tafiye-tafiyen mutanen 6 bisa zargin ta'addanci

Hukumomin kasar Faransa sun kwace takardun izinin tafiye-tafiye na wasu mutane 6, da ake zargin suna yunkurin zuwa kasashen Syria da Iraqi don bayar da tallafi ga mayakan Islama.

MAYAKAN ISIS
MAYAKAN ISIS
Talla

Ministan harkokin wajen kasar Bernard Cazeneuve, ya ce ana kuma shirin haramta wa wasu mutane 40 ficewa daga kasar.

Wannan ne karon farko da aka dauki irin wannan matakin, bayan da aka gabatar da shi a matsayin wani bangaren sabuwar dokar yakin da ta’addanci da aka gabatar a watan Nuwamban bara.

Ministan harkokin waje Bernard Cazeneuve ya ce in har Faransawa za su je Iraqi ko Syria su kai hari, to za su iya zama babbar barazana da za su iya kai muggan hare-hare a lokacin da suka dawo gida.

Mutanen 6 da aka karbe takardun izinin tafiye tafiyen nasu za su ci gaba da zama a cikin Faransa, bayan watanni 6 kuma a duba yuwuwar mayar musu, ko a ci gaba da rikewa.

Cazeneuve ya kuma bayya kokarin da ma’aikatar shi ke yi, na samar da hanyoyin da ‘yan uwa da abokai za su iya kai rahoton wanda suke zargi zai iya zama barazana ga al’umma.

Ministan ya ce an sami rahotanni fiye da dubu 1, inda kuma suka yi amfani da su waje hana mutane da dama yin tafiye tafiye zuwa kasashen Syria da Iraqi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.