Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnatin Gurguzu ta tsallake kuri’ar yankan kauna

‘Yan majalisar dokokin Faransa sun kada kuri’ar amincewa da Gwamnatin kasar ta ‘yan gurguzu inda aka mayar da hankali da sauye sauyen gwamnatin na tattalin arziki. ‘Yan majalisa 234, akasarinsu ‘yan jam’iyyun adawa ne suka kada kuri’ar rashin amincewa da gwamnati, sai dai wannan adadin bai kai abin da ake bukata don rusa gwammnatin ba.

Shugaban Faransa François Hollande tare da Firaminista Manuel Valls.
Shugaban Faransa François Hollande tare da Firaminista Manuel Valls. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

An fara shirin zaben gwada farin jinin gwamnatin ne, bayan da Firaminista Manuel Valls ya yi yunkurin yin amfani da tsarin mulki, wajen shigar da wasu sauye sauye a bangaren tattalin arziki, ba tare da amincewar ‘yan majalisa ba, lamarin kuma da ba a saba gani ba.

Mr. Valls ya dauki wannan matakin ne, sakamakon fargabar rashin amincewa daga ‘yan jam’iyyar shi ta gurguzu wanda zai iya dakile yunkurin sauye sauyen, da yanzu suka zama doka sakamakon rashin nasarar kuri’ar rashin amincewa da gwamnatin.

Gwamnatin tace sauye sauyen suna da muhimmanci, wajen bai wa ‘yan kasashen waje damar shiga a dama da su a harkokin tattalin arzikin faransa, da shine na 2 mafi girma tsakanin kasashen masu amfani da kudin Yuro.

Dama dai tattalin arzikin na Faransa na jan kafa, yayin da rashin aikin yi ke ci gaba da yawaita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.