Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Yau za’a fara sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya ta Ukraine da Rasha

Yau juma’a ne ake sa ran ci gaba da wani zagayen tattaunawar zaman lafiya, da ake yi domin kawo karshen rikicin kasar Ukraine

Des militaires ukrainiens dans les rue de Marioupol après des bombardements, le 24 janvier 2015, dans l'est de l'Ukraine.
Des militaires ukrainiens dans les rue de Marioupol après des bombardements, le 24 janvier 2015, dans l'est de l'Ukraine. REUTERS/Nikolai Ryabchenko
Talla

Za a yi ganawar ne a birnin Minsk babban birnin kasar Belarus, tattaunawar kuma za ta sami halartar wakilan kungiyar hadin kan kasashen Turai da na Rasha.

A cikin wata sanarwar da ta fitar, ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Belarus ta ce, hukumomin Ukraine sun bayyana aniyar gudanar da taron sasanta rikicin a yau Juma’a.

Sanarwar na zuwa ne jim kadan bayan da shugaban kasar ta Ukraine Petro Poroshenko ya nemi a gaggauta ganawa da ‘yan awaren masu goyon bayan Rasha, don kawo karshen zub da jinin da ake yi a gabashin kasar.

Poroshenko ya ce yana fatan taron na yau, zai kawo karshen rikicin cikin gaggawa, tare da janye muggan makaman da aka girke a yankin, kamar yadda aka tsara a wata yarjejeniyar ta watan Satumba.

A makon daya gabata jagoran ‘yan tawayen ya fice daga wata tattauanawar, ya kuma bayar da sanarwar ci gaba da kai hare hare, don kama wasu karin yankunan.

Taron da aka yi ranar 24 ga watan Disamba a birnin na Minsk ya gagara samar da wata mafita kan rikicin na Ukraine, inda jin kadan da gudanar da shi wani sabon rikicin ya sake barkewa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.