Isa ga babban shafi
Fransa

Majalisar Dattawan kasar Faransa ta amince da Kasar Falasdinu

Rahotanni daga kasar Faransa na cewar a karshen Makon nan ne majalisar Dattawan Faransa ta amince da kasar Falasdinu tare da yin kira ga gwamnatin Francios Hollande da ta amince da ‘yancin Falasdinawa bayan da tuni karamar Majalisar kasar ta amince da kudirin Dokar yin hakan

giovannisrights.wordpr...
Talla

Kudurin Dokar samun ‘yancin Falasdinawa, ya samu amincewar babbar majalisar Faransa ne da rinjayen kuri’u 153, yayin da wasu 146 suka kada kuri’ar kin amincewa.

Bayan amincewa da kudurin Dokar, Majalisar ta yi kira ga gwamnatin kasar Faransa da ta amince da kasar Falasdinu tare da jagorantar tattaunawar sulhu tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, bayan da karamar Majalisar kasar ta Faransa ta amince da kasar Falasdinu

Faransa dai ta bi sahun kasashen Spain da Birtaniya da Sweden da suka amince a ba Falasdinawa ‘yanci, inda kasashen ke ganin ita ce hanyar samar da zaman lafiya tsakanin Falasdinu da Isra’ila.

A shekarar 2012 shugaba Francois Hollande ya bukaci kafa kasar Falasdinu, tare da yin kira ga Isra’ila, ta daina gine-gine a yankunan Falasdinawa.
A shekarar 2014 ma Faransa ta bukaci kasashen duniya da su magance rikicin Isra’ila da Falasdinu cikin shekaru 2.

Tuni Isra’ila ta yi watsi da matakin tana mai cewa zai kara lalata yunkurin komawa Teburin tattaunawar sasanta rikicin gabas ta tsakiya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.