Isa ga babban shafi
Netherlands

Holland ta haramta shigo da Kaji

Gwamnatin kasar Holland ta haramta shigo da Kaji a cikin kasar bayan samun bullar cutar murar tsuntsaye da kan iya shafar mutane. Kaji kimanin 150,000 ne gwamnatin Holland tace zata kashe domin dakile bazuwar cutar zuwa ga mutane.

Jami'an kiwon lafiya suna aikin daukar matakan kariya domin kaucewa yaduwar cutar murar tsuntsaye
Jami'an kiwon lafiya suna aikin daukar matakan kariya domin kaucewa yaduwar cutar murar tsuntsaye Reuters
Talla

A wata gonar kaji ne aka samu bullar cutar ta murar tsuntsaye. Cutar kuma takan kashe kaji nan take kuma barazana ce ga mutane musamman masu kula da hidimar kajin.

Nau’in Cutar murar tuntsaye da ake kira H5N1 ta kashe sama da mutane 400 a yankin kudu masu gabacin Asia tun fara samun bulluwar cutar a 2003.

Haka kuma wata na’uin cutar da ake kira H7N9 ta kashe mutane sama da 170 tun daga 2003 zuwa yanzu. Akan haka ne kuma gwamnatin Holland ta dauki matakin haramta shigo da kaji da kwayakwayi na tsawon sa’o’I 72.

Akwai kuma aikin gwaji da za’a gudanar a sauran wuraren da ake kiwon kaji domin dakile bazuwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.