Isa ga babban shafi
Faransa-Birtaniya

Kasashen Faransa da Britaniya zasu kera kuramen jiragen yaki

Kasashen Faransa da Britaniya sun kaddamar da wani shirin hadin gwiwa, inda zasu duba yuwuwar kera kuramen jiragen saman yaki. Shirin da aka bayyana a matsayin wani tsarin da zai kawo sauyi a amakaman yakin sama, ya biyo bayan wata yarjejeniyar da kasashen 2 suka kulla ne, a yayin bukin nunin jiragen sama da aka yi a yankin Farnborough cikin wannan shekarar.An baiwa wasu kamfanoni 2 kwangilar gudanar da binciken da za a shafe shekaru 2 ana yi, kuma aikin zai lakume kudin daya kai YURO miliyon 150, wato kusan dalar Amurka Miliyon 190.Kasashen na Faransa da Britaniya za kuma su kara bayar da wani tallafin na YURO miliyon 100, cikin lokacin da za a gudanar da aiki.Cikin wata sanarwar hadin gwiwar da suka fitar, kamfanonin BAE Systems da Dassault Aviation, masu agudanar da aikin, sun ce wannan hadin kai na matsayin babbar hanyar samar da ci gaban makaman yaki na sama, tare da samar da hadin kai a bangaren tsaro tsakanin kasashen Faransa da Britaniya. 

Wani samfurin kurman jirgin sama
Wani samfurin kurman jirgin sama ©MINDEF/DGA
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.