Isa ga babban shafi
Turkiya

An sa Dokar hana fita a yankin kudancin Turkiyya

A jiya Laraba rundunar sojin Turkiya ta sa Dokar hanna fita a yankin kudancin kasar, hakan dai ya biyo ne bayan mutuwar mutane 19 a sakamakon zanga-zangar da kurdawa suka yi game da rashin katabus akan hare-hare da ake kai musu akan iyakar Siriya ta birnin Kobane

L'armée turque a pris position sur les hauteurs de Kobane. Mais elle n'intervient pas.
L'armée turque a pris position sur les hauteurs de Kobane. Mais elle n'intervient pas. REUTERS/Umit Bektas
Talla

Cigaba da yaki tsakanin kurdawa na barazana ga tabbatar da zaman lafiya a kan iyakar siriya, wanda kuma ya kasance wata babbar barazana ga makwabciyar kasar wato Turkiyya.

An dai yi itifakin cewar sanya Dokar hanna fita a gabashin kasar syriya zai taimaka wajen tsaigaita wuta a yakin da ake fama dashi da yanzu ke bukatar daukar mataki.

Gwamnatin Jami’iya mai mulki ta justice and development Party, ta ce bata yi amfani da karfin soja ba, wajen yakar masu da’awar kafa Daular islama ta ISIS da ke neman kwace Kobane.

Wanna hare-hare da ake kaiwa na yin tasiri matuka, dalilin da ya sanya sojoji turkiya baza tsaro a tituna da unguwanni Diyarbakir, Mardin da kuma Van da ke makwabtaka da siriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.