Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa za ta yi fama da gibin kasafin kudi nan da shekaru 3 masu zuwa

Gwamnatin Kasar Faransa mai fama da dimbin matsalolin tattalin arziki, ta fidda alkalumman cewar za ta fuskanci babban gibi a kasafin Kudinta nan da shekaru 3 masu zuwa. Gwamnatin ta sanar da hakan ne bayan da ta gabatar da tauyayyen kasafin kudinta na wannan shekarar

free-picture.net
Talla

Da yake karba tambayar manema labarai Ministan kudin kasar Michel Sapin ya fada cewar kasafin kudin kasar zai ci gaba da zama na gaba-gaba ga kankanta daga cikin kasafin kudin kasashen Nahiyar Turai har ya zuwa shekarar 2017.

Kasar dai ta dora alhakin hakan daga halin da daukacin yankin kasashe masu amfani da Kudin Euro yake ciki da kuma tashin farashin kayayyaki.

Ita dai kungiyar tarayyar Turai ta kayyade cewar ya zama wajibi ga kasa ta tabbatar ta tsayar da karfin tattalin arzikinta akan mizanin da bai wuce na kashi 3 daga cikin adadin yawan karfin tattalin arzikin yankin na Nahiyar Turai ba, kuma Faransa na iya kai ga matsayin ne kawai nan da shekarar 2017 kan hasahenta na sama da kashi 2.

Kasar Faransa dai ta yi alwashin cimma mizanin da ake bukata nan da shekara mai zuwa amma kuma rashin sanin tabbas da kasar ke fuskanta ya sa da wuya ta iya cimma hakan a cikin shekaru 2 masu zuwa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.