Isa ga babban shafi
Tarayyar Turai

Yan ajalisar kungiyar tarayyar turai na tantance sabin Kwamishinonin kungiyar

Yar kasar Suidin Cecilia Malmstom wace zata shugabanci sashen dake kula da hadahadar kasuwanci na kungiyar tarayyar turai ce, a jiya litanin ta buda soma karba tambayoyin kokof da yan majalisar kungiyar tarayyar turai suka gabatar mata, domin tantance sabin mambobin da zasu halarci majalisar comishinonin da zasu yi aiki da shugaban hukumar zartarwar kungiyar Jean Claude Juncker

REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Matsayin da Cecilia zata rike a kungiyar nada matukar muhimmanci, ga makomar tattalin arzikin nahiyar ta Turai, domin itace zata kula da rikitaciyar yarjejeniyar sakin mara ga harakokin kasuwanci tsakanin turai da kaashen Amruka da Canada ne, da aka jima ana ja’inja a kai

Yan majalisar dokokin tarayyar ta turai dai, zasu kai har ranar 7 ga watan October gobe, suna yiwa sababbin comishinonin kungiyar ta tarayyar 27 da shugaban hukumar zaratarwata Jean Claude Juncker ya gabatar masu

Ana ganin yan majalisar sun zabi su farawa ne da Cecilia ganin irin muhimmancin da matsayin da take takara a kai yake da shi ga ci gaban kasashen na turai kan hada hadar kasuwanci

Sai dai kuma tuni masu sharhi ke cewa babban abinda ya haifar da tantancewar ta kokof bai rasa nasaba da kwankwnton da ake yi cewa daga cikin sababin kwamishinonin da junkar ya gabatar domin tantancewa akwai wadanda baza su iya tafiyar da matsayin da aka dorasu a kai Ba

Ita dai Cecilia Malmstom ta yi rawar gani wajen amsa tambayoyin da yan majalisar na turi suka yi mata rubdugu dasu, musamman kan huldar nan mai tsini, ta sakin mara a tsakanin kasashen turai da kasashen Amruka da Canada, wace har yanzu aka kasa saka kawo karshenta
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.