Isa ga babban shafi

Jagoran neman 'yancin Scotland yace zai yi murabus

Jagoran neman ‘yancin kasar Scotland Alex Salmond yace zai yi murabus, bayan da ‘yan kasar suka kada kuri’ar ci gaba da zama karkashin mulkin Britaniya. Salmond, daya amince da shan kaye a zaben raba gardaman da aka gudanar ranar Alahamis data gabata, yace zai sauka daga mukamin nashi, da kuma jagorancin jam’iyyar SNP mai neman ‘yancin kan kasar, a watan Nuwamba mai zuwa.A halin da ake ciki kuma Sarauniya Elizabeth II, ta nemi ‘yan kasar su mutunta junan su, bayan yakin neman zaben daya rarraba kanun jama’a. 

Jagoran neman 'yancin Scotland, Alex Salmond
Jagoran neman 'yancin Scotland, Alex Salmond REUTERS/Russell Cheyne
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.