Majalisar Faransa na nazarin ayyukan Gwamnatin kasar
Majalisar Dokokin kasar Faransa ta gudanar da zama na musamman a yau talata domin jefa kuri’ar amincewa ko kuma rashin amincewa da salon siyasar Firaministan kasar Faransa Manuel Valls.
Wallafawa ranar:
Cikin jawabin da ya gabatar a gaban ‘yan Majalisar, Valls ya ce zai ci gaba da aiwatar da sauye-sauye domin farfado da tattalin arzikin kasar Faransa, ya kuma bukaci goyan bayan daukaci yan Majalisar wata hanyar ceto tattalin arziki kasar daga durkushewa.
Gwamnatin Faransa na fuskantar suka daga bangarori daban-daban na yan siyasa dama kungiyoyin kwadagon kasar da cewa ta kasa cika alkawuran da ta dauka a baya, ta bangarorin samarwa matasa ayyukan yi dama kawo daidaito a fuskar tattalin arziki kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu