Isa ga babban shafi
Faransa

Ma'aikatan kamfanin jiragen saman Faransa sun fara yajin aiki

Kamfanin Sufurin jiragen sama mallakin kasar Faransa Air France, yace ya zama masa dole ya soke tashin rabin jiragen sa, saboda yajin aikin da matuka jiragen zasu fara yau. Ma’aikatan na yajin aikin ne don nuna adawa da shirin kanfanin na rage yawan kudaden da yake kashewa.Daraktan ayyukan kanfanin Catherine Jude, tace kashi 48 kawai na jiragen kanfanin ne zasu yi aiki Litinin, ganin akalla kashi 60 na matukan sun sanya hannu kan takardar zuwa yajin.Kanfanin ya bukaci wadanda suka sayi tikitin kanfanin dan tafiye tafiye daga yau 15 ga wata zuwa 22 da su jinkirta tafiyar su har zuwa wani lokaci.Kungiyar matuka jiragen ta kira yajin aikin na mako guda, wanda zai zama irin san a farko tun shekarar 1998. 

wasu jiragen saman kamfanin Air France
wasu jiragen saman kamfanin Air France Reuters/Charles Platiau
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.