Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Rasha da Ukraine suna zargin juna kan sabon rikici

Kasashen Ukraine da Rasha na nuna wa juna dan yatsa, kan alhakin sabon rikicin daya barke a kasar ta Ukraine, bayan bangarorin 2 sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta. Hukumomin birnin Kiev sun zargi Rasha da kokarin kawar da Ukraine, bayan rikicin da aka fafata a kokarin da kasashen 2 ke yi, na karbe ikon wani filin jirgin sama a gabashin kasar ta Ukraine.Sai da Rasha ta zargi Amurka da kitsa rikicin da aka gwabza jiya Asabar, a daidai lokacin da sabbin takunkuman da kasashen yamma suka kakaba wa Rashan ke fara aiki.Rasha ta sake zafafa rikicin, bayan da ta tura ayarin motoci 220, zuwa yankunan dake hannun ‘yan tawayen na Ukraine, da tace kayan agaji ne, sai dai masu sa ido na kasashen Turai, da sojojin Ukraine basu samu sun duba abinda ke cikin motocin ba. 

'Yan tawaye masu goyon bayan Rasha a Ukraine
'Yan tawaye masu goyon bayan Rasha a Ukraine Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.