Isa ga babban shafi
EU-Rasha

Takunkumin Turai akan Rasha ya fara aiki

Kungiyar Tarayyar Turai ta soma aiki da wasu sabbin jerin takunkumin kariyar tattalin arziki da ta kakabawa kasar Rasha, duk da gwamnatin Rasha tace zata mayar da martani musamman ga batun wanzar da zaman lafiya a Ukraine.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da  Petro Poroshenko na Ukraine da Francois Hollande a Brussels
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tare da Petro Poroshenko na Ukraine da Francois Hollande a Brussels REUTERS/Guido Bergmann
Talla

Kasashen na Turai sun dauki matakin ne akan Rasha saboda ci gaba da bayar da goyon bayan da ta ke yi ga ‘yan tawayen da ke yakar gwamnatin Ukraine

Sabbin takunkumin sun shafi kamfanonin mai da tsaro da haramtawa bankunan Rasha yin hada-hadar kudi a kasuwar Turai.

Kuma sabbin takunkumin sun shafi wasu manyan na hannun damar Shugaban Rasha Vladimir Putin wadanda aka rufe asusun ajiyarsu tare da haramta ma su shiga kasashen kungiyar Turai.

Sai dai kuma kasashen na Turai sun bayyana cewa a shirye suke su dage takunkuman idan Rasha ta bayar da hadin kai nan da karshen watan Satumba.

A na sa bangaren shugaban kasar Amruka Barrack Obama ya bayyana kara daukar wasu sabbin takunkuman kariyar tattalin arziki a fannin makamashi da kuma tsaro a kan kasar Rasha bisa rawar da kasar ke takawa a rikicin Ukraine.

Yanzu haka kuma kasar Rasha tace ta tsara sabbin takunkumin da zata kakaba akan kasashen Turai da Amurka da suka hada da haramta shigo da motocin da aka yi amfani da su.

Kamfanin Dillacin labaran Rasha ya ruwaito wani na hannun damar shugaban kasar Vladimir Putin yana cewa bangaren ci gaban tattalin arzikin kasar ya tsara sabbin takunkumi akan kasashen yammaci.

Andrei Belousov yace akwai wasu kayyakin da ba su shafi abinci ba da kasashen yammaci ke dogaro da Rasha wadanda suka hada da motocin da aka yi amfani da su da tufafi.

Kasar Rasha tace tana iya dogaro da kanta ba lalle sai ta dogara da kasashen na Turai ba.

A watan jiya ne Rasha ta haramta shigo da kayan abinci daga Amurka da kasashen Turai domin mayar da martani ga takunkumin da suka kakaba ma ta tun da farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.