Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Sojin Rasha na kara yawa a kasar Ukraine

Wasu kungiyoyin kare hakkin bil’adama a kasar Ukraine sun zargi kasar Rasha da baza sojinta a cikin kasar, inda suka bayyana cewa a cikin watanni 2 da suka gabata yawan sojojin Rasha a kasar sun kai dubu 15

thedenverchannel.com
Talla

Kungiyoyin da ke kare hakkin dan adam a yankin gabashin kasar Ukraine inda ake tabka fada tsakanin ‘yan aware da Dakarun gwamnatin Kiev, sun bayyana cewa Kimanin Dakarun Rasha dubu 15 ne yanzu haka kasar ta tura a cikin kasar Ukraine a watanni 2 da suka gabata.

Inda suka ce an kuma kashe wasu da dama daga cikinsu a gumurzun da ake tabkawa tsakanin ‘yan aware masu goyon bayan Rasha, da Dakarun Gwamnatin kasar Ukraine da ke samun goyon bayan kasashen turai.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam din sun kara da cewa, yanzu haka Dakarun Rasha dubu 7 zuwa dubu 8 ne ke cikin kasar ta Ukraine.

Sun dai tabbatar da hakan ne daga Iyalan sojojin na Rasha bayan da suka daina jin duriyar dangin nasu ta wayar Tarho.

Mme Melnikova ma’aikaciya ce a sashen da ke kula da jama’a na ofishin Ministan tsaron kasar Rasha ta bayyana cewa, yanzu haka akwai kwamandojin sojin kasar ta Rasha da dama da ke gudanar da wasu ayukan soji na sirri a cikin kasar ta Ukarain.

Tuni dai mahukuntan Ukraine da kasashen turai suka zargi Rasha da ci gaba da jibge sojojinta a yankin gabashin Ukraine, zargin da a kullum Rashar ke musantawa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.