Isa ga babban shafi
Rasha-EU-Ukraine

Rasha ta nemi a kirkiro sabuwar kasar daga Ukraine

Shugaban kasar Rasha Vladamir Putin ya bukaci a gudanar da taro gaggawa domin kirkiro da wata sabuwar kasar a gabashin Ukraine, inda ya ce ta hakan ne kawai za a kawo karshen rikicin da ake fama da shi a yankin. Wannan ne karo na farko da shugaban na Rasha ya fito karara, ya bayyana matsayinsa na ganin an kirkiro sabuwar kasa daga cikin Ukraine, domin kawo karshen wannan rikici da ke ci gaba da haddasa takun-saka a tsakanin manyan kasashen duniya.Putin wanda ke amsa tambayoyi a cikin wani shirin talabijin da aka gabatar a jiya lahadi, ya bayyana cewa akwai bukatar gaggauta gudanar da wannan taro domin samar da sabuwar kasar, kuma haka ita ce mafita domin biya wa mazauna yankin kudu maso gabashin Ukraine bukatunsu ta warewa.A can baya dai batun bai wa mazauna yankin gabashin Ukraine wadanda mafi yawansu na magana ne da harshen Rashanci kwarya-kwaryan ‘yancin cin gashin-kai, shi ne babban abin da Rasha ke bukata, to amma sabbin kalaman na Vladamir Putin, na nuni a zahiri cewa Rashan na fatar ganin an raba kasar Ukraine.Sai dai a wani taro da ta gudanar karshen mako, Kungiyar tarayyar Turai ta EU, ta bai wa Rasha sabon wa’adi na mako daya, ko dai ta kawo karshen shishshigi a al’amurran cikin gidan Ukraine, ko kuma a kakaba ma ta sabbin takunkuman karya tattalin arziki. 

Shugaban kasar Rasha,  Vladimir Putin.
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin. Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.