Isa ga babban shafi
Turkiya

An rantsar da Erdogan a matsayin shugaban kasa

A kasar Turkiya an rantsar da Firaministan kasar Recep Tayyip Erdogan a matsayin shugaban kasa bayan ya shafe shekaru yana jagorantar gwamnati a kasar. Erdogan mai shekaru 60 ya karbi rantsuwar wa’adin shugabanci ne na shekaru biyar a birnin Ankara inda kuma ya sha alwashin gina sabuwar Turkiya ta hanyar yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima da samar da ayyukan ci gaba.

Friministan Turkiya  Recep Tayyip Erdogan
Friministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan REUTERS/Umit Bektas
Talla

Erdogan wanda ya shafe shekaru yana rike da mukamin Firaminista a kasar, ‘yan adawa suna zarginsa da yin salon mulkin danniya. Yayin da a lokacin rantsar da shi wakilan Jam’iyyar adawa ta Republican People Party suka fice zauren majalisa

‘Yan adawa dai suna zargin Erdogan ne da keta kundin tsarin mulki, musamman batun rashawa da ya daibaibaiye jam’iyyarsaa.

Erdogan ya lashe zaben shugaban kasa ne a ranar 10 ga watan Agusta da rinjayen kuri’u kashi 52. Kuma zai karbi ragamar shugabanci daga hannun Abdallah Gul wanda yanzu suke takun saka a Jam’iyyarsu ta AKP.

Bikin rashar da Erdogan dai ya samu halartar shugabannin kasashen gabacin Turai da Afrika da kasashen Asiya ba tare da halartar manyan kasashen yammacin Turai ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.