Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka-Rasha

Kasashen yammacin duniya sun yi Allah wadai da agajin da Rasha ta kai Ukraine

Kasashen yammacin duniya sun yi Allah wadai da motocin da Rasha ta tura dauke da kayan agaji zuwa yankin Lugansk, dake hannun ‘yan tawaye a gabashin kasar Ukraine. Hukumomin kasar ta Ukraine sun bayyana matakin a matsayin kutse a cikin kasarta, yayin da Amurka da kungiyar taraiyyar Turai suka gargadi hukumin birnin Moscow su gaggauta janye ayarin motocin da suka kai kayan agajin.Amuraka tace matakin zai iya sanadiyyar karin sabbin takunkumi ga kasar ta Rasha, yayinda da kwamitin tsaro na Majalisar Dinkun Duniya ya bayyana fargabar matakin zai iya dagula rikicin da aka shafe watani 4 a yi a kasar ta Ukraine. 

shugaban kasar Rasha , Vladimir Putin,
shugaban kasar Rasha , Vladimir Putin, REUTERS/Alexei Nikolskyi/RIA Novosti/Kremlin
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.