Isa ga babban shafi
Faransa

Ebola: Ma’aikatan Air France sun ki hawa jiragen da ke jigila a Yammacin Afrika

Kamfanin Jiragen sama na Air France yace wasu daga cikin ma’aikatansa sun ki hawa jiragen da ke safara zuwa kasashen Guinea da Saliyo da Najariya da ke fama da cutar Ebola. Kakakin kamfanin yace wasu daga cikin ma’aikatan sun ki yarda su tafi kasashen da cutar Ebola ta zama alakakai.

Jiragen Air France-KLM
Jiragen Air France-KLM REUTERS/Charles Platiau
Talla

Kodayake, hakan bai sa an dakatar da jiragen kamfanin zuwa kasashen ba.

Jiragen Air France na zuwa kasashen Yammacin Afrika fiye da duk wani daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama a duniya.

Kakakin Kamfanin Jirgin air France ya tabbatar wa Kamfanin dillacin labaran Faransa cewa, wasu ma’aikatan da ke yin hidima a cikin Jiragen da ke jigila a Yammacin Afrika sun kauracewa aiki.

Tuni dai jirgin British airways na Birtaniya da jirgin Emirate suka dakatar da yin jigila a kasashen Guinea da Saliyo, amma Air France ya ba Ma’aikatansa zabi a jiglarsa zuwa biranen Conakry da Freetown da Lagos.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin duniya tace cutar ta kashe mutane 84 a cikin kwanaki uku, abinda ya kawo adadin wadanda suka mutu sakamakon kamuwa da cutar Ebola zuwa 1,229.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.