Isa ga babban shafi
Turai-Rasha

Takunkumin Rasha ya yi tasiri akan Turai

Kungiyar Tarayyar Turai, ta ce za ta dauki wasu matakai na musamman domin taimaka wa manoman kasashen yankin wadanda aka tilasawa dakatar da shigar da kayan abinci zuwa kasar Rasha sakamakon takunkuman da aka kakaba wa kasar.

Vladimir Putin Shugaban Rasha yana zantawa da Sergei Lavrov Ministan harakokin wajensa
Vladimir Putin Shugaban Rasha yana zantawa da Sergei Lavrov Ministan harakokin wajensa REUTERS/Paulo Whitaker
Talla

Kwamishinan ayyukan noma na Kungiyar Tarayyar Turai ya ce a cikin makon gobe ne za su sanar da irin matakan da suke shirin dauka domin ceto manoman da yanzu haka suka tsinci kansu a cikin mawuyacin hali, sakamakon yadda aka hana su shigar da kayan gona a kasar Rasha ba tare da an yi masu tanadin wanda za su rika cinikayya da shi ba.

Kwamishinan ya ambacin nau’in manoman da tallafin zai shafa da suka hada da manoma barkono da kabeji da Tomatur da dai sauransu, amma abu ne mai wuya masunta su amfana da wannan tallafi a cewar wata majiyar.

Kungiyar ta ce ko baya ga batun samar da tallafi, dole ne a yi kokarin samar wa manoma da sabuwar kasuwa a maimakon Rasha, amma a halin yanzu za a yi amfani da wani asusun ko-takwana ne mai kunshe da Euro milyan 420 domin soma agazawa manoman da kawo yanzu suka yi tsimin dubban ton na abinci a cikin rumbunansa.

A cikin makon da ya gabata ne dai kungiyar ta Tarayyar Turai ta yi koyi da kasar Amurka, wajen sanyan sabbin takunkumai akan Rasha. Inda kuma Rasha ta mayar da martani na haramta shigo da kayan abinci a cikin kasarta daga kasashen Turai da Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.