Isa ga babban shafi
Ukraine-Malaysia

An fara zaman makoki sakamakon hatsarin jirgin Malaysia

A wannan laraba al’ummar kasar Netherlands na gudanar da zaman makoki sakamakon mutuwar mutanen kasar 193 a hatsarin jirgin saman kasar Malaysia da ya faru sararin samaniyar kasar Ukraine.

Aikin binciken gawarwakin fasinjojin jirgin Malaysia da ya fado a Ukraine
Aikin binciken gawarwakin fasinjojin jirgin Malaysia da ya fado a Ukraine REUTERS/Maxim Zmeyev
Talla

Yau ne dai za a isa da gawarwarkin mutanen kasar da suka mutu a hatsarin bayan an zakulo su daga cikin tarkacen jirgin.

Yanzu haka dai kasashen duniya na ci gaba da yin tir da kuma Allah wadai dangane da wannan lamari da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 298 daga kasashen duniya 10.

A ranar talatar da ta gabata ma Kungiyar Tarayyar Turai da kasar Canada, sun sanar da sanya sabbin takunkumai a kan Rasha, saboda alakarta da ‘yan tawayen Ukraine da ake zargi da hannu wajen harbo jirgin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.