Isa ga babban shafi
Ukraine-Malaysia

Aikin binciken hatsarin jirgin saman Malaysia a Ukraine

Jirgin kasa dauke da gawarwakin mutane 282 da aka zakulo daga tarkacen jirgin saman Malaysia da ya yi hatsari a Ukraine, ya tashi daga garin Torez da ke karkashin kulawar ‘yan tawaye inda hatsarin ya faru zuwa birnin Kharkiv da ke karkashin ikon gwamnatin Ukraine.

Jirgin kasa dauke da gawarwakin wadanda suka mutu a hatsarin jirgin Malaysia
Jirgin kasa dauke da gawarwakin wadanda suka mutu a hatsarin jirgin Malaysia
Talla

Za a dai mika gawarwakin wadannan mutane ne a hannun hukumomin kasar Holland inda wannan jirgi ya taso kafin ya yi hadari kamar dai yadda Firai ministan kasar Malaysia Najib Razak ya sanar.

‘Yan tawaye dai sun amince da tsagaita wuta a fili mai fadin kilomita 10 daga inda hatsarin ya faru domin bai wa masu bincike damar gudanar da ayyukansu.

A yau talata Kungiyar Tarayyar Turai na gudanar da taro domin duba yiyuwar kakaba wa kasar Rasha sabbin takunkumai na tattalin arziki dangane da irin goyon bayan da take bai wa ‘yan tawayen na Ukraine wadanda ake zargi da harbo jirgin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.