Isa ga babban shafi
Rasha-Ukraine-Amurka

Rasha na fama da matsin Lamba kan kakkabo Jirgin Malaysia

Kasashen duniya sun yi wa kasar Rasha caa akan ta tursasawa ‘Yan tawayen Ukraine su bari a shiga yankin da Jirgin Malaysia ya tarwatse, yayin da Amurka tace Rasha ce ta ba ‘Yan tawayen Ukraine Makami mai linzami da suka harbo jirgin

Des inspecteurs de l'OSCE, accompagnés  des miliciens séparatistes ukrainiens pro-russes, inspectent les débris du vol MH17 de la Malaysian Airlines à Grabovo dans la région de Donetsk, le 18 juillet 2014.
Des inspecteurs de l'OSCE, accompagnés des miliciens séparatistes ukrainiens pro-russes, inspectent les débris du vol MH17 de la Malaysian Airlines à Grabovo dans la région de Donetsk, le 18 juillet 2014. REUTERS/Maxim Zmeyev
Talla

‘Yan tawaye masu kishin kasar Rasha da suka mamaye gabascin Ukraine sun ce sun gano bakin Akwatin nadar bayanai na jirgin Malaysia wanda ya tarwatse da daukacin mutanen da ke cikinsa a yankin da suke iko, kuma sun ce a shirye suke su mika wa tawagar masu bincike Akwatin bayan sun kwashe gawwakin mutane kimanin 200 a inda jirgin ya fadi.

Amurka ta yi zargin Rasha ce ta ba ‘Yan tawayen makami mai linzami da suka harbo jirgin.

Manyan kasashen Turai Faransa da Birtniya da Jamus sun yi gargadi ga Rasha ta tursasawa ‘Yan tawayen Ukraine su ba masu bincike damar isa ga yankin da Jirgin ya tarwatse, idan ba haka ba su tsaurara wa Rasha Takunkumi.

Ana zargin ‘Yan tawayen na Ukraine da boye wasu hujjoji da za su tabbatar da harbo jirgin Malayasiya aka yi da makami mai linzami.

Birtaniya tace lokaci ya yi da Rasha za ta cire hannunta ga sha’anin Ukraine, tare da yin kira ga Shugaba Putin na Rasha ya daina marawa ‘Yan tawaye baya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.