Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka-Rasha

Majalisar dunkin Duniya ta ce a binciki faduwar Jirgin Malaysia a Ukraine

Hukumar tsaro ta Majalisar dunkin Duniya ta bukaci gudanar da cikakken bincike akan yanda aka karbo Jirgin jigilar kasar Malaysia a yankin gabashin Ukraine da ya hallaka Mutane 298

ojhsspartanchronicles.com
Talla

Wannan kiran dai ya faru ne a wani taron gaggawa da Hukumar tsaron Majalisar dunkin Duniyar ta kira inda wakilan kasashe daban daban da hatsarin ya shafa suka gabatar da jawabbansu na alhini da bukatar yin cikakken bincike

Jakadiyar kasar Amurka a Majalisar dunkin Duniya ta bayana cewar idan har zargin da ake yiwa ‘yan tawaye masu samun goyon bayan kasar Rasha a wannan hatsarin ya tabbata, to lallai ne su dauki alhakin harin, kuma muhimmin abu ne a fara bincike ba tare da bata lokaci ba.

Akan haka taron ya yanke shawarar cewar ya zama wajibi dukkanin wadanda abin ya sha kama daga Rasha da ‘yan tawaye masu goyon bayanta da kuma kasar Ukraine, su bada hadin kai ta hanyar tsagaita buda Wuta, domin samun damar kwararru masu bincike na kasa-da-ka su isa su yi bincike akai.

Jami’an kula da lafiyar Jiragen Sama dai sun sanar da cewar an tabbatar da lafiyar Jirgin jigilar kasar Malaysian nan da ya fadi a yankin gabashin kasar Ukraine tare da kashe Pasinjoji 298 da ke cikinsa.

Mataimakin shugaban kungiyar tarayyar Turai Huib Gorter ya bayyana cewar dukkanin Na’urorin Jirgin na aiki kamar yanda ya kamata a lokacin da ya tashi.

Ya zuwa yanzu dai wannan hatsarin jirgin ne mafi muni da aka taba samu a jiragen da ke tashi daga kasar Netherlands tun bayan na shekarar 1977 da ya kashe Jamusawa 238 a yankin Tenerife na tsibirin Canary sa’adda jirage 2 kirar Boeing 747 suka yi karo da juna abinda ya yi sanadin mutuwar mutane 582.

An ce dai kwararru sun yiwa Jirgin garambawul a Kuala Lumpur kasar Malaysia a Makon jiya kuma an tabbatar da lafiyar Jirgin kamin ya tashi harma da lokacin da yake tafiya.

Jirgin dai ya hallaka mutane ciki kuwa hadda Glenn Thomas mai magana da yawun Hukumar Lafiya ta Majalisar dunkin Duniya da ke kan hanyarsa ta zuwa Melbourne kan ziyarar aiki.

Faduwar Jirgin dai ya haifar da kacce-nacce musamman tsakanin kasar Amurka mai bayyana cewar harbo Jirgin aka yi sakamakon fadan da ake tsakanin ‘yan tawayen kasar Ukraine masu samun goyon bayan kasar Rasha da kuma Dakarun kasar ta Ukraine a yyain da kasar Rasha da ake gani da alhaki ke cewar ba gaskiya ba ne.

Daukacin bangarorin biyu dai na nunawa juna Yatsa akan daukar alhakin kakkabo Jirgin da ya kona daukacin mutanen da ke ciki.

Ana dai ci gaba da bayyana sunayen mutanen da ke cikin Jirgin da kuma sunayen kasashen da suka fito, inda kassahen da suka samu mutanensu a ciki ke cewar za su bi diddigin yadda hatsarin ya auku.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.