Isa ga babban shafi

Rasha ta nemi Ukraine ta janye dakarunta a yankin Gabas

Rasha ta jajirce sai kasar Ukraine ta janye dakarunta a yankin Gabashin kasar domin a dakile yaduwar rikicin a sauran sassan kasar. 

Dakarun Ukraine a yankin Gabashin kasar
Dakarun Ukraine a yankin Gabashin kasar
Talla

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ta fitar a yau Laraba, ta ce janyewar dakarun Ukraine a gabashin kasar da kuma zaunawa domin a tattauna, zai taimaka wajen shawo kan rikicin.

Har ila yau ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Rasha ta nuna mamakin ta kan yadda hukumomin Kiev da Amurka suka yiwa yarjejeniyar Geneva mummunar fassara.

An dai kwashe fiye da wata guda ana rikici a gabashin kasar ta Ukraine inda ‘yan tawaye dake da muradin hada kai da Rasha suka mamaye gine ginen gwamnati a garuruwa Doneskt da Luganks.

A kuma makon da ya gabata ne kasashen Amurka da Rasha da Ukraine hade da kungiyar tarayyar Turai suka cim ma yarjejeninyar bukatar a kawo karshen rikicin gabashin kasa, lamarin da ya cutura.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.