Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka

Joe Biden na ziyarar aiki ta yini biyu a Ukraine

Mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden ya isa birnin Kiev na kasar Ukraine domin gudanar da ziyarar aiki, a daidai lokacin da magoya bayan kasar Rasha ke ci gaba da yin garkuwa da wasu muhimman cibiyoyin gwamnati a gabashin Ukraine.  

Вице-президент США Джо Байден в аэропорту Борисполя, 21 апреля 2014, Украина
Вице-президент США Джо Байден в аэропорту Борисполя, 21 апреля 2014, Украина REUTERS/Valntyn Ogirenko
Talla

Ziyarar ta tsawon kwanaki biyu, a lokacinta Mista Biden zai gana ga shugaban riko na Ukraine Olexandre Tourt-chinov da firaministansa Arseni Iatsenyuk, wadanda ke ci gaba da neman samun goyon bayan kasashen duniya a takun sakar da suke yi da kasar Rasha tun bayan balllewar yankin Crimea.

Wannan dai ita ce ziyarar da wani babban jami’in Amurka ya kai a Ukraine tun bayan wadda sakataren harkokin waje John Kerry ya kai birnin Kiev a ranar 4 ga watan Maris da ya gabata.

Ana dai kallon wannan ziyara a matsayin wani kwarin gwiwa ga hukumomin kasar ta Ukraine, wadanda ke zargin Rasha da marawa ‘yan aware baya a birane da dama da ke gabashin kasar, yayin da kuma Amurkar ke barazanar kafa sabbin takunkumai akan kasar ta Rasha nan ba da jimawa ba.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da manyan kasashen duniya suka ce sun cimma yarjejeniya kan yadda za a warware wannan rikici a siyasance, To sai dai ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, ya zargi hukumomin Kiev da yi wa yarjejeniya kafar angulu, ta hanyar shirya kai farmaki kan ‘yan aware.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.