Isa ga babban shafi
Cyprus

MDD ta zargi Cyprus da rashin baiwa bakin haure cikakkiyar kariya

Hukumar dake kula bakin haure a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, ta zargi kasar Cyprus, wacce mamba ce a karkashin Kungiyar Tarayyar Turai da rashin bayar da cikakkiyar kariya ga bakin haure dake neman mafaka a kasar.

Bakin haure kasar Syria da yaki ya daidaita
Bakin haure kasar Syria da yaki ya daidaita Reuters/Antonio Parrinello
Talla

A cewar hukumar, ta yi mamakin yadda kasar ta Cyprus ta jingine dokar da ta ba da damar a kare bakin haure da suka fito daga kasashen da ake yaki.

“Mun yi matukar mamakin kan yadda kasar ta Cyprus ta jingine dokar dake ta ba da damar a baiwa bakin haure kariya.” Damtew Dessalegne, wakilin hukumar ya ce.

A cewar Dessalegne akwai dokar da Kungiyar Turai ta samar kan yadda mambobin kungiyar za su baiwa bakin haure gudunmuwa wajen hada iyalansu wacce kasar ta Cyprus ta kawar da idonta akai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.