Isa ga babban shafi
Ukraine-EU-Rasha

Hollande da Cameron sun jaddada goyon bayansu ga Ukraine

Shugaban Francois Hollande na Faransa da Firaministan Birtaniya David Cameroon, sun yi kakkausar suka dangane da yadda ‘yan bindiga da ke goyon bayan kasar Rasha ke ci gaba da tayar da hankula a garuruwa da dama na gabashin kasar Ukraine.

Cincirindon mutane wajen ginin gwamnati a birnin Donestk
Cincirindon mutane wajen ginin gwamnati a birnin Donestk REUTERS/Maks Levin
Talla

Shugabannin biyu sun bayyana haka ne a birnin Paris lokacin da suka gana a yau litinin.

A sanarwa da ta fitar jim kadan bayan shugabannin biyu sun gana, fadar Elysees ta shugaban Faransa ta ce bayyana hare-hare da kuma yin garkuwa da muhimman gine-ginen gwamnatin kasar Ukraine da ‘yan bindigar suka yi wani abin assha ne, wanda kuma bai kamata kasashen duniya su ci gaba da zura ido hakan na faruwa.

David Cameroon da Francois Hollande, sun kuma bayyana cikakken goyon bayansu ga gwamnatin kasar Ukraine, tare da yin kira ga kasar da ta ci gaba da aiwatar da sauye-sauye na siyasa da ta yi wa al’umma kafin gudanar da zaben shugabancin kasa a ranar 25 ga watan Mayu mai zuwa.

A tsawon kwanaki biyu da suka gabata, wasu daruruwan mutane da ke goyon bayan kasar Rasha sun tsananta kai hare-hare da kuma kwace wasu muhimman cibiyoyin gwamnatin Ukraine a yankin gabashin kasar, lamarin da kasashen yammacin duniya ke cewa kasar Rasha na da masaniya a kai.

To sai dai shugaban riko na Ukraine Olexandre Tourtchinov, ya bayar da umurnin kaddamar da farmaki domin kwato wadannan yankuna a hannun mutane da ya kira su suna ‘yan ta’adda.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.