Isa ga babban shafi
Ukraine

Jagorar 'yan adawar Ukraine Tymoshenko ta shiga yajin cin abinci

Jagorar 'yan adawa sannan tshohuwar Fira ministar kasar Ukraine Ioula Tymoshenko, ta fara yajin cin abinci domin nuna bacin ranta dangane da gazawar gwamnatin kasar na kulla alakar cinikayya da Kungiyar Tarayyar Turai.A makon jiya ne dai kasar Ukraine ta yi ba zata inda ta ki sanya hannu cikin yarjejeniyar wanda shi ne mataki na farko kafin a yi na’am da ita cikin kungiyar.  

Masu zanga-zangar goyon bayan Ioulia Timochenko.
Masu zanga-zangar goyon bayan Ioulia Timochenko. REUTERS
Talla

Masu fashin baki na ganin cewa ba karamin koma baya ne ba ga kungiyar kasashen Turai mai wakilai kasashe 28, wadda ta kunshi wasu kasashe da dama da ke karkashin kominisanci ae tsakiyar Turai da suka taba kasancewar karkashin Russia.

Steve Blockmans na cibiyar nazarin tsare-tsaren Turai da ke Brussels, ya ce shigar da Ukrain cikin kungiyar na da dimbin alfanu.

Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai Herman Van Rompuy da kuma Shugaban Hukumar kasashen na Turai Jose Manuel Barroso na dora laifin jinkirin ne ga kasar Russia, inda suke fadin cewa batun shigar da Ukaraine cikinsu dai na nan ana tattaunawa.

Ita dai kasar Ukraine ta dora jinkirin da aka samu ne ga harkokin tsaron kasa, amma kuma masu fashin baki na ganin jinkirin ya samo asali ne saboda fargabar barazanar da Shugaban Russia ya yi na cewa ana iya daukar matakan ladabtarwa muddin Ukraine ta shiga kungiyar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.